1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai wa shugaban Venezuwela hari

Gazali Abdou Tasawa
August 5, 2018

Shugaban Venezuwela Nicolas Maduro ya ketara rijiya da baya bayan da wasu suka yi yinkurin halaka shi a jiya Asabar lokacin da yake halartar wani bikin faretin sojoji a birnin Caracas.

https://p.dw.com/p/32dU8
Nicolas Maduro
Hoto: picture-alliance/epa/Miraflores Presidential Palace

Shugaban Venezuwela Nicolas Maduro ya ketara rijiya da baibai bayan da wasu suka yi yinkurin halaka shi a jiya Asabar ta hanyar kai masa hari da wasu jirage maras matuka dauke da bama-bamai lokacin da yake halartar wani bikin faretin sojoji a birnin Caracas. 

A cikin wata sanarwa da ministan sadarwa na kasar Jorge Rodriguez ya fitar inda ya sanar da afkuwar lamarin ya ce sojoji bakwai sun ji rauni a cikin harin inda yanzu haka ana can ana jinyarsu a gida asibiti.

Tuni dai Shugaba Maduro ya zargi Shugaba Juan Manuel Santos na Kwalambiya da kuma 'yan kasar ta Venezuwela mazauna Amirka da kitsa wannan yinkuri na kashe shi da ya ci tura. Sai dai kuma shugaban kasar Kwalambiyan ya musanta zargi yana mai cewa ba shi da tushe balantana makama.

Sai dai kuma wata bakuwar kungiyar tawaye wacce ta kunshi fararan hula da sojoji ta dauki alhakin wannan harin da aka kai wa Shugaba Nicolas Maduro