Shugaba Kenyatta ya gana da Odinga | Labarai | DW | 09.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Kenyatta ya gana da Odinga

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta da madugun adawa Raila Odinga, sun ce sun kawo karshen tsamin dangantakar da ke tsakaninsu, wanda ya samo asali daga sa-in-sar da ta biyo babban zaben kasar na bara.

Bildkombo Kandidaten Wahlen Kenia 2017

Shugaba Kenyatta da madugun adawa Raila Odinga

A karon farko Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya gana da madugun adawan kasar Raila Odinga, inda suka ce sun kawo karshen tsamin dangantakar da ke tsakaninsu da ya samo asali daga sa-in-sar da ta biyo babban zaben kasar na bara. Lokacin wata ganawar da suka a wannan Juma'a, shugaba Kenyatta ya shaida wa taron 'yan jaridu a Nairobi babban birnin kasar cewa sun fahimci juna, inda suka amince za su hada kai saboda ci gaban al'umarsu.

Madugun adawar kasar Raila Odinga wanda da ma ke kalubalantar sakamakon zaben da ya bai wa shugaba Uhuru Kenyatta nasara, ya ce lokaci ne ya yi na mayar da wuka kube. Odinga da ya rantsar da kansa a matsayin shugaban al'umar Kenya cikin watan Janairu, ya ce sun yi watsi da duk wasu bambance-bambancen da za su iya ruguza kasar ta su, suka kuma kaiga matakin da suka dauka.