1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi wa fursunoni afuwa a Ruwanda

Abdul-raheem Hassan
September 15, 2018

Madugun 'yar adawa a Rwanda da wani fitaccen mawakin kasar na daga cikin mutane sama da 1,000 da gwamnatin Ruwanda ta yi wa sakin talala daga zaman gidan yari.

https://p.dw.com/p/34tv0
Ruanda vor den Wahlen 2017
Shugaban kasar Rwanda Paul KagameHoto: picture-alliance/dpa/G. Ehrenzeller

Victoire Ingabire da ke zaman shekaru 15 a kurkuku bisa zarginta da ta jagorantar kungiyar FDU ba bisa ka'ida ba, an ba da damar fitar da ita nan take tare da wasu fursunoni.

Fitaccen mawakin kasar Ruwandan Kizito Mihigo da aka tsare shekaru hudu bisa zargin kitsa kashe shugaban kasar, na cikin wadanda aka yi wa sakin talala.

'Yanta fursunonin da Shugaba Paul Kagame ya yi, ya biyo bayan wata takardar bukatar afuwa da fursunonin suka rubutawa gwamnati a watannin baya.