1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Jammeh ya tsige jikadodi 12

Gazali Abdou Tasawa
January 9, 2017

Shugaba Jammeh na Gambiya ya sabke jikadodin 12 na kasarsa a kasashen ketare wadanda suka bukaci da ya mika mulki ga Adama Barrow sabon zabebben shugaba.

https://p.dw.com/p/2VXMp
Gambia Yahya Jammeh Präsident
Hoto: Reuters/C. G. Rawlins


Rahotanni daga kasar gambiya na cewa Shugaba Yahya Jammeh ya sabke jakadun kasar 12 na kasashen ketare da suka hada da na MDD da kasashen Amirka, Senegal, Chaina, Rasha Birtaniya, Turkiyya. Ministan harakokin wajen kasar ta Gambiya ne ya bayyana sunayen jakadodin wadanda nan take aka bukaci su dawo gida ba tare da bayyana dalillan daukar wanann mataki ba. 

Sai dai wata majiya ta ofishin ministan harakokin wajen kasar ta Gambiya da ta bukaci a sakaya sunanta ta kwarmata wa kamfanin dillancin Labaran Faransar na AFP cewa matakin ba zai rasa nasaba ba da kiran da wadannan jakadodin suka yi wa Shugaba Jammeh a cikin wata wasika da suka rubuto masa a karshen watan Disamba inda suka bukaci da ya sabka da kan mulki tare da mika shi ga Adama Barrow wanda hukumar zaben kasar ta bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar.