Shugaba Jammeh na son tazarce a Gambiya | Labarai | DW | 28.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Jammeh na son tazarce a Gambiya

Shi dai shugaba Jammeh mai shekaru 50 da haihuwa da ke jan ragamar wannan karamar kasa da ke a Yammacin Afirka ana masa kallo na dan kama karya.

Yahya Jammeh

Shugaba Yahya Jammeh

Shugaban kasar Gambiya Yahya Jammeh wanda ke kan karagar mulkin wannan kasa shekaru 21 zai sake tsayawa takara a karo na biyar a zaben da kasar za ta yi a watan Disamba kamar yadda rahotanni na kafar talabijin a kasar ta Gambiya suka nunar.

Shi dai shugaba Jammeh mai shekaru 50 da haihuwa da ke jan ragamar wannan karamar kasa da ke a Yammacin Afirka ana masa kallo na dan kama karya tun bayan da ya karbi mulki bayan wani juyin mulki a shekarar 1994.

Takarar shugaban dai ta samu amincewa ta jam'iyyar AFPRC tun a ranar Juma'a sai dai ba a kai ga bayyanawa ba sai a yammacin ranar Asabar a cewar gidan talabijin na kasar ta Gambiya.

Kasar ta Gambiya me alumma kimanin miliyan biyu kashi casa'in cikin dari na zama Musulmi yayin da kashi takwas cikin dari ke zama Kirista kashi biyu kuma masu bin addinin gargajiya. shugaban kasar Jammeh na shan sukar 'yan fafutika da kasashen Yamma ko da a shekarar 2010 sai da kungiyar EU ta tsaida tallafin Euro miliyan 22 da za ta ba wa kasar saboda batutuwa da suka shafi take hakkin bil Adama.