1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya ƙaddamar da taron ƙasa

March 17, 2014

Wakilai 500 ne daga kowace ƙusurwa za su tafka mahawara kan makomar ƙasar na tsawon kwanaki 90 dan baiwa shugaba shawarwari kan hanyoyin warware rigingimun da suka addabe ta

https://p.dw.com/p/1BRBp
Nigeria Goodluck Ebele Jonathan Komitee zur Vorbereitung der Nationalen Konferenz
Hoto: DW/U. Musa

A wani abun dake zaman kama hanyar bude sabon babi ga tarrayar Najeriya dake shirin sabuwar dari a ciki fata na cigaba, da yammaciyar yau shugaban kasar Goodluck Ebele Jonathan ya kaddamar da babban taro na kasa Abuja.

Dattawa da ragowar masu fada a jin kasar 500 ne dai suka dau damara da nufin tinkarar muhimman kalubalen da ke tarnaki ga kokarin kasar na ci-gaba a cikin wani babban taron da gwamnatin kasar ke yi wa kallon kafa ta kaiwa ga tudun muntsira.

Taron da ke zaman na 11 a cikin tarihin kasar na shekaru dari dai a fadar shugaban kasar na zaman sabon fatan dinkewa waje guda da nufin dora kasar a bisa sabon babi na cigaban al'umma da siyasarta.

Nigeria Abuja Nationalrat
Tsoffin shugabanin NajeriyaHoto: DW/U. Musa

“Ba zamu iya hada hannu tare mu gina kasa da tunani iri guda ba, in har muna kallon juna da tsana da kiyyayya a tsakanin junanmu. Matsaloli na jiya su kare a jiya. yau na zaman sabon yayi, kuma wannan taro na zaman dan ba ta sabuwar Najeriya. Wannan dama ce ta tunani sabo, dole ne kuma muyi watsi da tunanin baya da aka gina a bisa kiyyaya da takara ta ba gaira a tsakanin al'ummominmu daban-daban.”

Karkashin jagorancin tsohon babban alkalin kasar Mai sharia Idris legbo Kutigi dai 'yan taron za su share kwanaki har 90 suna muhawara da junansu a bisa jeri na batutuwan da suka shafi batun siyasa da ma tsari na gwamnati da rabon arziki dama 'yanci na gashin kai duk dai da nufin shawo kan matsalolin fatara da talauci da mummunan rashin tsaron da yai katutu a kasar.

Ƙalubalen mabanbantan ra'ayoyi

To sai dai kuma tun ba'a kai ga ko'ina ba ra'ayi ya kai ga gidan ban-ban a tsakanin masu muhawarar da ke kallon taron da idanu daban daban da kuma kila ke shirin yanke hukunci abisa nisan hangen nasu. Dr Junaidu Mohammed dai na zaman daya a cikin wakilan al'ummar jihar kano guda ukun dake zauren taron.

“Daga wannan hautsinin da muka gani jiya da kuma wanda muka tarar yau banga abun da wannan taro zai tsinana ba. Zamu zo aikin banza muyi wahalar banza akashe kudin talaka a banza mu watse a banza babu bukatar talakan da za'a warware”

To sai dai in har ana shirin shan shayi a kai ga watsewa ba tare da kaiwa ga biyan bukatar yan kasar dake neman sauyi ba a tunanin su Junaid, ga dan uwansa Ibrahim Nasiru Mantu da ya fito daga jihar Plateau wai jiki magayi ga yan kasar da ke cikin yanayi maras kyau

protestierende Menschen in Nigeria
Jami'yyun adawa na yawan zanga-zangaHoto: DW/Uwais Abubakar Idris

“Duk mutumin dake kasar nan ina jin ko makaho ne shi yana gani, in kurma ne yana ji, in ma bebe ne yana magana saboda abubuwan sun lalace sun yamutse fiye da yadda ake tsammani, babu wanu bangaren najeriya da yake wurin tsira, ya zama kamar tashin kiyama ko'ina babu wurin tsira, saboda haka kowa yaga uwar bari watakila zamu tsaya nan mu gaya kanmu wurin tsira.”

Wakilai sun kwatanta taron a matsayin damar faɗar gaskiya

Kokarin na fadawa juna gaskiya ko kuma kokari na amfani da taron wajen biyan bukatar rai dai an bude taron ne tare da mahalarta taron tsayawa bisa tsohuwar akidar rabuwar data dauki shekara da shekaru tana zama ummul' abaisin rabuwar kasar bisa kudu da arewa. King Alfred Diete Spiff dai na zaman basaraken gargajiyar Brass a jihar Bayelsa mai takama da arzikin man fetur, kuma a fadar sa yana zauren taron ne da nufin tabbatar da burin al'ummarsa na mallakin man fetur din da Allah ya saka a kasar su.

“ A sashi a doka cewar duk wani arzikin da ka samu a wurinka to zaka hakoshi da taimakon baki na waje in hali yayi, sai ka biya gwamnatin tarrayar Najeriya haraji. Ta haka ne kowace jiha zata kara himma da kuma hobbasa.”

To sai dai kuma an kai ga bude taron ba tare da hallartar daukacin gwamnoni dama wakilan jami'iyyar APC ta adawa 16 dake kallon taron a matsayin bata lokaci da dauke hankali na gwamnati.

Mawallaf: Ubale Musa
Edita: Pinaɗo Abdu Waba