1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba China Hu ya fara ziyarar aiki ta yini uku a nan Jamus

Mohammad Nasiru AwalNovember 11, 2005

A ranar farko ta wannan ziyara shugaba Hu ya gana da shugaban tarayyar Jamus Horst Köhler a birnin Berlin

https://p.dw.com/p/Bu4J
Shugaba Hu a Jamus
Shugaba Hu a JamusHoto: AP

Shugaban China Hu Jintao da takwaransa na Jamus Horst Köhler sun yi fatan karfafa tuntubar juna tsakanin Jamus da China. A dangane da haka a yau shugaba Hu Jintao zai ajiye harsashen aikin ginin wata cibiyar yada al´adun China ta farko a Jamus.

“Ya kamata mu inganta huldar dangantaku tsakanin mu don ci-gaban kasashen mu.”

Sannan shi kuma shugaba Köhler sai ya dora yana mai cewa:

“Ina bukatar ganin an kakkafa cibiyoyin tuntubar juna tsakanin Jamus da China don ba al´umomin kasashen mu ba kawai shugabannin ba damar tuntubar juna.”

Köhler ya yabawa nasarar da gwamnatin birnin Beijing ke samu wajen yaki da talauci a cikin kasar.

“A kowace shekara China na samun nasara kubutar da miliyoyin mutane daga ukuba ta talauci. Wannan nasara na da muhimmanci ga duniya baki daya. Hakan kuma na nuni da fa´idar da ke tattare cikin sabuwar alkiblar siyasa da China ta dauka. Muna cirawa hukumomin kasar hannu bisa wannan gagarumin aiki da suke yi.”

To duk da haka dai shugaban na Jamus yayiwa gwamnatin China hannunki mai sanda dangane da matakan keta hakkin dan Adam a cikin kasar. Ya ce tattalin arziki na bunkasa ne idan aka samu ´yanci da walwalar jama´a.

“Mun san cewar komai na da lokacinsa haka kuma mun fahimci cewar China ka iya yin gaban kanta. To amma sanin kowa ne cewar dukkan al´umomin wannan duniya ta mu na da muradin zama cikin ´yanci da walwala, kamar yadda aka zayyana a cikin kudurin MDD.”

A ranar farkon ziyarar ta yini 3 da yake kawowa Jamus shugaban na China ya sanya hannu kan yarjeniyoyi da dama na inganta huldar tattalin arziki. Alal misali gwamnatin birnin Beijing zata saye sabbin jiragen kasa na zamani na kare gudunka har guda 60 daga nan Jamus. A cikin shekarun nan dai huldar cinikaiya tsakanin Jamus da China na ci-gaba da bunkasa yayin da kasuwannin China mai samun bunkasar tattalin arzki na kimanin kashi 9 cikin 100 a shekara ke dada jan hankalin kamfanonin Jamus.

To amma duk da haka huldar diplomasiya ba ta tafiya kamar yadda ake so. Alal misali shugabar gwamnati mai jiran gado Angela Merkel ta ce zata ci-gaba da girmama takunkumin KTT na sayarwa China da makamai. A wani lokaci yau din nan shugaba Hu zai gana da Merkel da kuma Gerhard Schröder. Su kuwa a nasu bangaren shugabannin jam´iyun FDP da The Greens sun yi kira ne ga gwamnatin China da ta ba al´umarta cikakken ´yancin tafiyar da addini da kuma fadin albarkacin bakinsu ba da wata tsangwama ba, sannan sun yi kira ga sabuwar gwamnatin Jamus da ta fito karara ta yi magana game da keta hakkin ´yan dan Adam a kasar ta China.