Shugaba Chavez zai shiga tsakani don sakin waɗanda ake garkuwa da su a Columbia | Labarai | DW | 01.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Chavez zai shiga tsakani don sakin waɗanda ake garkuwa da su a Columbia

Shugabankasar Venezuela Hugo Chavez ya ce yana shirin tattaunawa da shugabannin ´yan tawayen Columbia a wani yunkuri na samun sakin wasu mutane da dama da ´yan tawayen ke garkuwa da su. Chavez ya bada wannan sanarwa ne bayan wani taro da yayi da takwaransa shugaban Columbia Alvaro Uribe a birnin Bogota. Ya ce zai gana da shugabannin ´yan tawayen a birnin Caracas amma bai fadi ranar da za´a yi wannan taro ba. shugaban na Venezuela ya je kasar Columbia ne don tattaunawa akan wata shawara wadda ke neman gwamnati ta yi musayar firsinonin ´yan tawaye da wadanda ake garkuwa da su. Wata fitattaciyar ´yar siyasar Columbia Ingrid Betancourt da wasu Amirkawa 3 na daga cikin mutanen da kungiyar ´yan tawayen FARC ke garkuwa da su.