Shugaba Buhari ya koma gida | Labarai | DW | 19.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Buhari ya koma gida

Bayan jinyar ciwon kunne na kusan makwanni biyu a London Shugaban na Najeriya ya koma gida inda ya samu tarba daga mukarrabansa

Shugaba Buhari da yammacin yau ya sauka filin jiragen saman Abuja cike da nishidi, yana ta jinjina wa ministoci da man'yan hafsoshin tsaro, wadanda suka je domin tarbansa. A ranar shida ga watan da muke ciki(06.06.2016), Shuagaba Buhari dan shekaru 73 da haifuwa ya tashi zuwa London domin likitocin su duba lafiyarsa, bisa shawarar da wasu likitoci suka bashi a Najeriya.