1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Buhari ya koma aiki da tarin kalubale

Uwais Abubakar Idris
August 21, 2017

Bayan komawar Shugaba Muhammadu Buhari gida da ya sanya murna da farin ciki na ganin kyautatuwar lafiyarsa, abin da ke zukatan mafi yawan ‘yan kasar shi ne kalubalen da ke fuskantar shugaban da ma kasar a yanzu.

https://p.dw.com/p/2iXT4
Nigeria Abuja -  Muhammadu Buhari nach Rückkehr aus England
Hoto: Reuters/Nigeria Presidency Handout

Duk da murna da farin ciki da a'lummar Najeriya ke yi a kan komawar shugaban nasu, batun matsaloli da ke shan kan gwamnatin da al’ummarta muhimmi ne a abubuwa da ke gaban shugaban na Najeriya.
Kama daga masu ikirarin ballewa don kafa kasarsu da ya ce ba za ta sabu ba, ya zuwa  kama hanyar kara sukurkucewar tsari kama daga hare-hare na ta’adanci ya zuwa masu garkuwa da jama’a duka matsaloli ne da ke gaban gwamnatin da ta yi wa alummar Najeriyar alkawarin samun canji, tamkar ra'ayin Injiniya Buba Galadima gogaggen dan siyasa a jamiyyar APC mai mulki.

Nigeria Präsident Muhammadu Buhari
Saukar shugaban da kwari ta sanya fata a zukatan 'yan NajeriyaHoto: picture alliance/AP Photo/S. Alamba

Masana harkokin siyasa na bayyana ra’ayoyi mabambanta a kan inda ya kamata shugaba ya maida hankali a sauran lokacin da ya rage mashi na mulki muddin shugaban Najeriyar na son kaiwa ga gaci. Kiraye-kiraye na masu son a sakewa Najeriyar fasali da jamiyyar APC ta yi ta maza har da kafa kwamiti zai zama abin da ka iya daukan hankalin shugaban kasar da ma zaben da ake fuskanta. Amma ga Mallam Abdurahman Abu Hamisu masani a fannin siyasa da ke cibiyar wanzar da zaman lafiya da ci gaban kasa ya ce akwai bukatar tsara inda aka dosa.

Nigeria Präsident Buhari Rückkehr
Buhari dai ya samu tarba ta girma a tsakanin 'yan kasaHoto: picture-alliance/Nigeria State House/S. Aghaeze

To sai dai sanin cewa shugaban na Najeriya ya kwashe fiye da rabin wa’adinsa kuma ga dimbin alkawuran da ya yi bai kai garesu ba ya sanya fara tunanin cewa anya da sauran lokaci kuwa musamman ganin yadda matasa ke nuna bukatar canji. 
A yayin da shugaban ke kara murmurewa kalaman farko da suka fito daga bakinsa na nuna kowa ya shiga taitayinsa, za’a tabbatar da hakan ne ga takun da zai yi a mulki musamman a kan wasu mukarabansa da ake ganin suna hana ruwa gudu.