Shugaba Buhari ya kai ziyara Maiduguri bayan harin Boko Haram | Labarai | DW | 12.02.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Buhari ya kai ziyara Maiduguri bayan harin Boko Haram

Shugaba Buhari ya isa Maiduguri kai tsaye daga kasar Habasha bayan kammala taron kolin kungiyar tarayyar Afirka.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai wata ziyarar ba zata a jihar Borno da ake ganin tana da nasaba da hare-haren da mayakan Boko Haram ke kaiwa a 'yan kwanakin nan musamman harin da suka kai garin Auno da mutane sama da 30 suka riga mu gidan gaskiya.

Shugaba Buhari wanda ya sauka a Maiduguri a wannan rana ta Laraba, kai tsaye daga kasar Habasha bayan kammala taron kolin kungiyar tarayyar Afirka, ya samu tarba daga gwamnan jihar Borno, inda suka yi ganawar sirri kafafin ayarin shugaban ya nufi cikin garin Auno.

Wakilinmu a Maiduguri Al-Amin Suleiman Muhammad ya ce babu tabbacin wuraren da shugaban zai ziyarta, sai dai jama'a na fatan ya je Auno ya ganewa kansa abin da ya faru da kuma ziyartar sansanonin 'yan gudun hijira.