Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin 2018 | Labarai | DW | 07.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin 2018

Kasafin Naira tiriliyan takwas da digo shida wato dala miliyan dubu 28 ne da aka gabatar ga majalisar dokokin Najeriya da kudiri na farfado da tattalin arzikin kasar a shekarar 2018.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a wannan rana ta Talata ya gabatar da kasafin kudi na Naira tiriliyan takwas da digo shida wato Dala miliyan dubu 28, kasafin da ya gabatar ga majalisar dokokin kasar mai kudiri na farfado da tattalin arzikin Najeriya a shekarar 2018.

A lokacin da shugaban ke gabatar da wannan kasafi a gaban zaman hadin gwiwa na majalisun kasar ya ce wannan kari ne na kashi 16 cikin dari idan aka kwatanta da na shekarar 2017, hakan kuma zai taimakawa wajen cika muradun gwamnati na farko wato a fannoni na tattalin arziki da suka hadar da samar da hanyoyi da kula da fannin lafiya da samar da gidaje da ayyukan yi.

Za a dora hasashen samun kudaden tafiyar da kasafin kan fitar da gangar danyan mai miliyan dubu biyu da digo uku a kowace rana, sabanin miliyan dubu biyu da digo biyu a shekarar da ta gabace shi, inda za a siyar da kowace ganga Dala 45. Shugaba Buhari dai ya ce burin gwamnatinsa shi ne cika alkawura da suka yi wa 'yan Najeriya.