Shugaba Bongo na iya tafiyar da mulki | Labarai | DW | 19.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Bongo na iya tafiyar da mulki

Fadar shugaban kasar Gabon ta bayyana cewa matsalar Shugaba Ali Bongo Ondimba ta rashin iya magana ta kau inda a yanzu yake iya tafiyar da harkokin mulkin kasar ba tare da wani shamaki ba.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar yayin taron manema labarai da ta gudanar. Matakin fitar da sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da kawancen 'yan adawa ke bayyana shugaban dan shekaru 60 da ke fama da rashin lafiyar shanyewar wani bangare na jiki, da cewa ba ya iya tafiyar da harkokin mulki.

Kwana guda gabanin sanarwar dai an hangi Shugaban Ali Bongo a bainar jama'a, yana dogara sanda a yayin da yake jagorantar bukin tunawa da ranar samun 'yancin kan kasar.