Shugaba Bashar al-Assad ya ce yana yaƙi da ′yan Al-Qaida | Labarai | DW | 19.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Bashar al-Assad ya ce yana yaƙi da 'yan Al-Qaida

Shugaban na Siriya ya ce ƙasarsa ba ta cikin halin yaƙi ya ce tana fuskantar farmaki ne daga 'yan ta'adda da ke neman tayar da zaune tsaye.

Assad ya bayyana haka ne a cikin wata Hira da gidan telbijan na Amirka FOXNEWS ya yi da shi. kafin daga bisani ya musunta sahihanci aikin bincike da sefetocin Majalisar Ɗinkin Duniya suka yi a kan zargin da ake yi cewar dakarunsa sun yi amfani da makamai masu guba a kusa da birnin Damascus a cikin watan jiya a faɗan da suke yi da 'yan tawayen.

Shugaban na Siriya ya ce a shirye yake a lalata makaman nasa masu guba amma ya ce abune da ke buƙatar kuɗi kana kuma zai ɗauki lokaci sannan ya ce idan Amirka za ta iya ta biya kuɗaɗen aikin. Yanzu haka dai ana ci gaba da samun rashin zutuwa a kan batun na Siriya tsakanin sauran ƙasashen duniya da Rasha wacce ke ɗora alhakin kai hare-haren a kan 'yan tawaye.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu