Shugaba Ashraf Ghani ya gargadi ′yan Taliban | Labarai | DW | 06.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shugaba Ashraf Ghani ya gargadi 'yan Taliban

Rahotanni daga Afganistan na cewa harin bam ya halaka mutane bakwai tare da jikkata wasu 15 a harabar wani masallaci da ke birnin Herat da ke kan iyaka da Iran.

Wannan hari na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun karuwar adadin mutane da suka mutu a harin bam din birnin Kabul a makon da ya gabata, daga 80 zuwa 150. Shugaba Ashraf Ghani ya gargadi mayakan da su amince da sulhu da zai tsaida zub da jini ko su ji a jikinsu. Shugaban ya yi wannan bayani ne a taron shugabannin kasashe 22 da ke taro kan zaman lafiya a birnin Kabul.

Sai dai wannan jan kunne ya samu martanin harbe-harben makamin roka daga 'yan tada kayar bayan a harabar taron, sai dai harin bai raunata kowa ba.

Birnin Kabul dai na cikin matakan tsaro tun bayan mummunan harin bam da aka kai da babbar mota, da ya yi sanadiyyar mutuwa da jikkata mutane da dama a kusa da ofisoshin jakadancin kasashen waje.