Shirye shiryen zaben sabon Paparoma | Labarai | DW | 01.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shirye shiryen zaben sabon Paparoma

Manyan limaman darikar roman katolika sun hallara a fadar Vatikan domin nazarin 'yan takara dake neman matsayin sabon Paparoma.

Cardinal cadinal na Roman Katolika daga sassa daban daban na duniya sun hallara a fadar Vatikan dake birnin Rome, domin fara shirye shiryen zaben sabon Paparoma. A wannan Alhamis din ce dai Paparoma Benedict na 16 yayi murabus daga shugabantar Churchin roman katolika a hukumance, wanda ya sa shi kasancewa paparoman farko da ya ajiye mukaminsa a tarihin majami'ar tun shekaru 700 da suka gabata. Taron manya manyan limaman katolikan, zai kuma kasance wata dama ce ta yin muhawara dangane da 'yan takara dake neman wannan matsayi na shugabantar 'yan darikar Katholik kimanin biliyan 1.2 dake fadin duniya. Ana saran cewar a tsakiyar wannan wata na maris ne shirin zai kankama. Bayan ranarsa ta karshe kuma mai susan rai a matsayin Paparoma a wannan alhamis, jaridu na kasashen duniya sun yabawa matakin da bajamushen mai shekaru 85 da haihuwa ya dauka, wanda a cewarsu zai kasance abun koyi ga duk wani Paparoma mai shekaru makamancin nasa a nan gaba.

Mawalafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Yahouza Sadissou Madobi