1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirye-shiryen zaben 2015 a Najeriya

December 11, 2014

A yayin da ya rage kasa da watanni uku a gudanar da manyan zabuka a Najeriya, manyan jam'iyyun siyasar kasar sun kammala zabukan tsayar da 'yan takara.

https://p.dw.com/p/1E2eL
Wahlen Nigeria Ergebnis
Hoto: AP

Jam'iyyar PDP da ta kwashe shekaru kimanin 15 tana jan ragamar mulki a kasar ta tabbatar da shugaban kasa Goodluck Jonathan a matsayin wanda zai tsaya mata takara a zaben na watzan Fabrairun 2015, yayin da tsohon shugaban gwamnatin mulkin sojin Najeriya Janar Muhammad Buhari mai ritaya ya samu tikitin tsaya wa jam'iyyar adawa ta APC takara.