1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin gudanar da zabubbuka a Taiwan.

Uamaru Aliyu / LMJJanuary 15, 2016

Ranar Asabar 16 ga watan Janairu ne al'ummar Taiwan za su kada kuri'unsu, domin zaben sabon shugabana kasa da 'yan majalisun dokoki.

https://p.dw.com/p/1HeRW
Dan takarar jam'iyya mai mulki ta KMT Eric Chu
Dan takarar jam'iyya mai mulki ta KMT Eric ChuHoto: picture-alliance/AP Photo/Ch.Ying-ying

Zaben kamar yadda masu lura da al'amuran yau da kullum suka nunar, zai zama 'yar manuniya a game da yadda shugaban kasa mai barin gado Ma Ying-Jeou ya tafiyar da wa'adin mulkin har sau biyu. 'Yan makwanni kalilan kafin zaben na shugaban kasa, jam'iyar da ke mulki mai suna Kuomintang ko kuma KMT a takaice, ta sanya 'yar takarar da ta tsayar, inda a maimakonta aka nada shugaban jam'iyar Eric Chu a matsayin dan takara.

Yayin da 'yan kasar ta Taiwan za'a su zabarwa kansu ba ma sabon shugaban kasa kadai ba, har da sabbin wakilan majalisar dokoki, idanun duniya ya fi tattara ne ga wanda za'a zaba kan mukamin shugaban kasar. Gaba daya dai 'yan takara uku ne masu wakiltar jam'iyu daban-daban za su nemi mukamin na shugaban kasa. Bayan shugaban jam'iyar da ke mulki ta Kuomintang, wato Erich Chu akwai kuma Tsai Ing-wen da ke wakiltar jam'iyar adawa ta demokradiyya, wato DDP da kuma James Song dan shekaru 73 daga jam'iyar PFP.

Yi wuwar samun shugaba mace

Ya zuwa yanzu dai ra'ayoyin jama'a da aka ji kafin zaben ya nuna cewar 'yar takara ta jam'iyar adawa Tsai Ing-wen ce ake sa ran za ta lashe zaben.

Macen da ake sa ran za ta lashe zaben Taiwan Tsai Ing-wen
Macen da ake sa ran za ta lashe zaben Taiwan Tsai Ing-wenHoto: picture-alliance/AP/W. Santana

Ko da shike cikin watan Oktoba jam'iyar da ke mulki ta Kuomintang ta maye gurbin mace 'yar takara da ta tsayar wato Hung Hsiu-chu saboda rashin isasshen farin jini, amma wanda ya maye gurbinta shugaban jam'iyar Eric Chu shi ma bai sami nasarar jan hankalin masu kada kuri'a ya zuwa gareshi ba. A ranar jajiberin zaben, dan takarar na jam'iyar Kuomintang ya gana da manema labarai inda yace:

"Abin da muka fi bai wa fifiko a kwanaki biyu na karshe kafin zaben shi ne kara tsananta kampe. Ina kuma bukatar goyon bayanku."

Taiwan ta samu ci gaba

Jam'iyar da ke mulki ta ce a tsawon shekaru takwas na shugaba mai barin gado Ma Ying-jeou kasar Taiwan ta sami ci gaba matuka, kuma an dauki matakai domin kyautata zaman jama'a da karfafa huldodi tsakanin Tsibirin na Taiwan da China. Wannan ma dai shi ne abin da dan takara daga jam'iyar PFP, James Soong ya mayar da hankali a kansa lokacin ganawa da 'yan jaridu, kwana guda kafin zaben na shugaban kasa.

Ya ce: "Idan aka zabeni zan ci gaba da tattaunawa tsakanin kasarmu da China, tare da mutunta juna da kuma sanin ya kamata. Tun a shekarun baya ma, kowa ya san cewar ni ne mutumin da aka danka masa alhakin kula da yadda dangantaka ta ke tsakanin Taiwan da China. Karbar mulkina zai tabbatarwa duniya cewar zaman lafiya da kwanciyar hankali za su ci-gaba da tabbata a wannan 'yanki. Za a kuma a ci-gaba da kiyayesu.

Dan takarar shugabancin kasa a taiwan James Soong
Dan takarar shugabancin kasa a taiwan James SoongHoto: picture-alliance/epa/D. Chang

Bayan zaben shugaban kasa, za kuma a kada kui'ar zaben 'yan majalisar dokoki, wadda tsahon shekaru 66 kenan jam'iyar Kuomintang ta ke da cikakken rinjaye a cikinta. Duk sabon shugaban kasar da aka zaba a kuri'un na ranar Asabar daga cikin 'yan takarar guda uku, za'a rantsar da shi ne ranar 20 ga watan Mayu mai zuwa.