Shirye-shiryen Kirsimeti a Najeriya | Siyasa | DW | 19.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shirye-shiryen Kirsimeti a Najeriya

Yayin da lokacin da bikin Kirsimeti ke gabatowa Shugabannin addinin Kirista sun bukaci gwamnati ta tabbatar da tsoro

Fargaba bisa yuwuwar kai harin kunar bakin wake ko tayar da bama-bamai da kai miyagun hare-haren a wuraren ibada da tashoshin mota da Kasuwanni da sauran wuraren gudanar da bukukuwan Kirsimti da shigowar sabuwar shekara.

Hakan dai ya sanya limaman majami'u da shugabannin addinin Kirista daga ko'ina janyo hankalin gwamnatin Tarayyar Nigeria da na jihohin wajen tabbatar da samar da jami'an tsaro a cikin kasar, domin dakile yiwuwar kai farmaki ko kunar bakin wake a majami'u da suka saba fuskanta a kowace shekara yayin Kirsimeti.

A cikin mako mai zuwa za a gudanar da bikin na Kirsimeti. Tuni dai gwamnatin Jihar Kaduna da rundunar 'yan sandar jihar suka fara shirye-shiryen daukar matakan wadata isasshen tsaro a lokacin wannan biki.

Sauti da bidiyo akan labarin