Shirye-shiryen binne zakara damben duniya Muhammad Ali | Labarai | DW | 06.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shirye-shiryen binne zakara damben duniya Muhammad Ali

An kai gawar tsohon zakaran damben duniya Muhammad Ali zuwa mahaifarsa domin shirye-shiryen binne shi a wannan Jumma'a da ke tafe.

Ana sa ran mashahuran mutane za su hallara a jawabai da za a yi domin tuna wa da shahararran tsohon dan damben duniya Muhammad Ali. Daga cikin manyan bakin da za su yi jawabi har da tsohon shugaban Amirka Bill Clinton da kuma dan wasan barkwanci Billy Crystal.

Shi dai Muhhammad Ali ya bar duniya yana da shekaru 74 da haihuwa, kuma ya kasance cikin shahararrun mutane a karni na 20 da ya gabata. Mutane da dama a duniya sun nuna juyayi da mutuwar ta Muhammad Ali.