Mali: Zaben shugaban kasa mai cike da fata
July 26, 2018Daga cikin 'yan takarar dai akwai Soumaïla Cissé wanda ke a matsayin babban mai kalubalantar shugaban kasa mai ci Boubakar Keita. Sai dai akwai fata mai yawa kan wannan zabe.
Babban abun da manyan kasashen duniya da ke da sojoji a kasar ta Mali tare da rundinar MINUSMA ke jira, shi ne na ganin an farfado da batun aiwatar da yarjejeniyar nan ta zaman lafiyar da aka cimma a shekara ta 2015 a tsakanin gwamnatin ta Mali da tsaffin 'yan tawayen kasar wadanda mafi yawansu Abzinawa ne.
Duk kuwa da wannan yarjejeniya da ka cimma, hare-haren 'yan jihadi na kara kamari a yankin arewacin kasar ta Mali da ma tsakiyar kasar da ke karkashin dokar ta-baci tun daga shekara ta 2015, da kuma wasu yankuna na Burkina Faso da na Jamhuriyar Nijar masu makwabtaka da kasar, inda rikicin ke rikidewa ya zuwa na tsakanin kabilu.