Shirin zuwa zabe a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya | Siyasa | DW | 23.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shirin zuwa zabe a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

A ranar Lahadi mai zuwa 27 ga watan Disemba al'ummar Afirka ta tsakiya ke kada kuri'ar zaben shugaban kasarsu tsakanin 'yan takara 30.

Kwanaki kalilan bayan zaben raba gardama kan kundin tsarin mulki, 'yan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya za su sake kada kuri'a a ranar Lahadi mai zuwa wato 27 ga watan Disemba, da nufin zaben sabon shugaban kasa da na kuma 'yan majalisa. Sai dai kuma har 'yan kasar ba su san manufofin 'yan takara ba.

Juye-juyen mulki da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta fiskanta tun bayan da ta samu 'yancin kanta shekaru 55 da suka gabata sun fi zabukan da aka gudanar a kasar a tsawon wannan lokaci yawa. Saboda haka ne 'yan kasar ke fatan cewar wadannan tagwayen zabukan su juya wannan babi tare da dora kasar kan kyakyawan tafarki. Sylvestre da ke aikin gwamnati a Bangui babban birni ya na daga cikin masu wannan ra'ayi.

"A shekaru 30 na baya-bayan nan ba wani sauyi da muka gani. Al'amura sun tabarbare a kasar nan. Fatanmu shi ne mu sami sauyi ta hanyar zaban shugaban da zai ciyar da kasar nan gaba."

'Yan Afirka ta Tsakiya sun jahilci alkiblar akasarin 'yan takarar

Sai dai kuma 'yan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ba su san wanda ya kamata su zaba a mstayin shugaban kasa a tsakanin 'yan takara 30 ba, saboda ba a san alkiblar da suka dosa ba. Hasali ma dai abin da ya faru a kuri'ar raba gardama zai sake maimata kansa, inda al'umma za su yi zaben tumin dare ta hanyar kada wa dan takara kuri'a ba tare da sanin manufofinsa ba.

Abin da dai kawai ya fito fili shi ne Shugaba Francois Bozize da aka hambarar a shekara ta 2013 ba zai sake dawowa kan karagar mulki ba, saboda kotun tsarin mulki ta yi watsi da takararsa, matakin da ya ce babu adalci a cikinsa.

"Wannan mugunta ce idan aka yi la'akari da mukamin shugaban kasa da na rike a baya na tsawon shekaru 10. Amma yanzu kuma aka ce ni ba komai ba ne. An mayar da ni saniyar ware."

Majalisar Dinkin Duniya ta zargi Bozize da marar hannu wajen ruruta wutar rikicin da ya barke a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, ta hanyar mara wa mayakan sa kai 'yan anti Bakala baya don far wa Musulmi.

Shekaru uku Kiristoci da kuma Musulmin suka shafe suna fada da juna, lamarin da ya haddasa salwantar da rayukan mutane miliyan hudu da dubu 700.

'Yan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na fatan ganin an yi zabe lafiya

Amma daga bisani a watan Janirun 2014 an kafa gwamnatin rikon kwarya wacce ta kunshi Kirista Catherine Samba Panza a matsayin shugaba, yayin da Musulmi Mahamat Kamoun ya zama Firaminista. Talakawan kasar dai ba su ga abin da gwamnati ta tsinana ba. Saboda haka ne Susanne stollreiter, jami'a a reshen kasar Kamaru na Gidauniyar Friedriech Ebert ta ce Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta sake samun karbuwa tsakanin takwarorinta na duniya ne idan sabon shugaba ya rungumi sabon salon mulki.

"Ana zamne kara zube a wannan kasa, fatan da ake da shi shi ne samun zababbiyar gwamnati da za ta iya yin gaban kanta, maimakon wacce za ta zama 'yar amshin shatar cibiyoyin kudi na duniya shigen gwamnatin rikon kwarya."

'Yan takara biyu ne ake sa rana za su taka rawar gani a zaben shugaban kasa: Na farko shi ne Martin Ziguele na jam'iyar MLPC wanda Kiritsa ne kuma ya taba zama firaministan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a shekarun 1990. Na biyu kuma shi ne Karim Meckassoua wanda Musulmi kuma tsohon minista ne. Abubuwan da 'yan takaran suka sa a gaba dai na kama da juna, su ne samar da zamna lafiya, sake gina kasa da kuma habaka tattalin arzikin Jamhuriyar Afirka Tsaakiya.

Sai dai kuma duk da cewar ana hasashen cewar jam'iyyar MLPC za ta iya samun kujeru da dama a majalisar dokoki, amma kuma tasirin da rikicin addini ya yi a kasar, ya sa har yanzu ba a san maci tuwon ba a zaben shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, sai miyar ta kare.