1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus sun mayar da hankali kan zuba jari a Afirka

Zainab Mohammed Abubakar
November 22, 2019

Batun son zuba jari a kasashen nahiyar Afirka da wasu kasashen Turai suka kuduri yi da kuma tashe-tashen hankula a yankin Sahel na daga cikin batutuwan da suka dauki hankulan jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/3TXur
Deutschland Berlin | Konferenz Compact with Africa | Angela Merkel, Bundeskanzlerin | Gruppenbild
Hoto: Reuters/F. Bensch

A labarinta mai taken "Dalilin da ya sa matsakaitan 'yan kasuwar Jamus ke muradin kara zuba jari a kasashen Afirka" Jaridar der Taggesspiegel ta ce wajen kamfanonin Jamus 600 ne membobi a kungiyar hadakar 'yan kasuwar Jamus da wannan nahiya. Ba kasafai kake jin wani labari mai dadi game da Afrika daga nesa ba. Ko mene ne dalili? Afirka dai nahiya ce mai girma wadda za a iya cewa ta kunshi komai da komai. 

Akwai kasashen da cin hanci da rashawa yai musu katutu, kana akwai kasashe da ke cikin yanayi mawuyaci na tashe-tashen hankula, sai daura da wannan matsaloli, ana iya bayyana Afirkan a matsayin nahiya mai bunkasa babu kakkautawa daura da gudanar da sauye sauye. Balaguro zuwa wadannan kasahen ne kadai zai bai wa mutum damar sanin cewar akwai abubuwan ban mamaki na cigaba da ke gudana, wadanda ko a nahiyar Turai ba zaka gansu ba.

A wannan makon ne dai shugabannin Afirkan suka gana da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a birnin Berlin karkashin tsarin nan na raya ci-gaban Afirka wato "Compact with Africa" da kasashen G20 suka fito da shi. Merkel ta jaddada manufar kara huldar kasuwanci da nahiyar. Manyan kasashe masu bunkasa a duniya a yanzu haka suna cikin matsaloli. Alal misali Rasha da Iran cikin takunkumi na tattalin arziki, a daya hannun kuma Amirka da China na cikin wani wadi na tsaka mai wuya na rashin jituwa a fannin kasuwanci. Domin haka ne aka karkata kan Afirka. 

Deutschland Berlin | Konferenz Compact with Africa | Angela Merkel, Bundeskanzlerin | mit Roch Marc Christian Kabore, Burkina Faso
Roch Marc Christian Kabore da Angela Merkel a yayin taron Compact with AfricaHoto: Reuters/J. MacDougall

Ita kuwa jaridar die Tageszeitung tsokaci tayi game da "Halin ni 'yasu" da yankin Sahel ke ciki na tashe-tashen hankula. Jaridar ta ce, kokarin da da kasashen duniya ke yi na yakar ayyukan tarzoma tamkar ana saka ne baya na warwara. A birnin Bamako fadar kasar Mali, mutane daga kabilu dabam-dabam maza da mata yara da manya sun mamye tituna suna zanga zanga. Mutane na dauke da kwalaye da ke cewar " Ni ma ina da abunda zan fada". Wanda ke nufin basu da damar tofa albarkacinsu a taron hadin kan kasa da gwamnati ta kira. 

Sai dai ba Malin kadai ce ke da wannan matsala ba, yankin na Sahel baki dayansa na cikin wadi-na-tsaka-mai wuyar fita. Daga Malin zuwa Burkina Faso da Nijar, hada da tabkin Chadi da Nigeriya da Kamaru da Chadi, miliyoyin mutane ne ke gudun hijira saboda karuwar hare haren 'yan ta'adda. Hare-haren kan iyaka na cigaba da gudana babu kakkautawa. Kamar za a iya cewar dabaru sun karewa jami'an tsaron idan aka kwatanta da yadda ayyukan tarzoman ke cigaba da ta'azzara. 

Daga batun rigingimu a yankin Sahel sai Kenya. A sharhin da ta rubuta mai taken " sabon arzikin man Kenya"  Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce, rigingimu ba sabon abu ba ne ga al'ummar arewacin Kenya. Sai dai watakila gano albarkatun mai zai taimaka wajen samar da zaman lafiya. Arewacin Kenyan mai kama da yankin Sahara, da ke kusa da tabkin Turkana, yanki ne da wuya a yi wata daya cur ba tare da an kai farmaki ba. Wani lokaci mayakan kabilar Turkana ke kai hari kan takwarorinsu na Pokot. A yayin hare haren akan sace shanu a wasu lokutan ma mata.