1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin zaben shugaban kasa a Faransa

Salissou Boukari
April 21, 2017

Yakin neman zabe ya dauki wani sabon salo a daidai lokacin da zaben na Faransa na ranar 23 ga watan Afrilu ke karatowa, inda wasu 'yan takara ke bin gida-gida don gamsar da masu zabe.

https://p.dw.com/p/2bhk5
Frankreich elf Präsidentschaftskandidaten treten in TV-Debatte gegeneinander an
Masu neman shugabancin kasar Faransa a zabe mai zuwa na ran 23 ga watan Afrilu 2017.Hoto: picture alliance/abaca/J. Domine

Wasu daga cikin magoya bayan dan takara Emmanuel Macron na bin gida-gida don jan ra'ayin wadanda basu gama tantance wanda za su zaba ba, hakan kuma ya yi kama da abin da ya faru kan Barrack Obama a shekarar ta 2008 lokacin da yake neman shugabancin Amirka. Christlle Derman wata matashiya ce 'yar shekaru 25 da haihuwa, yakin neman zabe ga Macron ya zame mata tamkar aiki na biyu baya ga ainahin aikinta da ta ke yi. Kusan kullum da safe sai ta bi jama'a ta na raba musu takardar yakin neman zabe kafin ta wuce wajan aikinta na sharhi kan lamuran siyasa.

Frankreich Präsidentenwahlen 2017
Jerin hotunan 'yan takara a zaben Shugaban kasar FaransaHoto: Reuters/C. Hartmann

Frankreich Die Linke vor der Wahl | Julien Wahlkampf
Masu bin gida-gida don neman gamsar da masu zabeHoto: DW/D. Pundy

Tawagar Macron ta shiga wata unguwa da a baya unguwar talakawa ce wadda a yanzu kuma ta sauya sosai, inda ake samun attajirai a cikinta. Unguwar ta na cikin gunduma ta 18 ne. Wata mata sanye da lullubinta cike da fara'a ta fito daga gidan ta, wacce ta ce ita ba 'yar Faransa ba ce amma kuma 'ya'yan ta 'yan kasar ne sai dai kuma kanana ne ba su kai suyi zabe ba amma wata rana idan sun girma za suyi zaben. A can gaba kuma wani gida ne, inda nan din ma dai wata mata ce ta fito daga ciki wacce ta ce ita har yanzu ba ta  gama yanke shawarar wanda za ta zaba ba. Ta ce mijin ta direban Taxi ne wanda yanzu haka ya rasa kusan kashi talatin na cininkin da yake, sannan ta kara da cewa zai yi matukar wahala ta amince ta zabi Macron sai in har sun mata bayani mai gamsarwa kan cewa Macron zai sanya tsarin kyautata yanayin walwala da jin dadin jama'a.

Lex Paulson wani dan Amirka ne ya na kuma daya daga cikin wadanda suka yi yakin neman zabe wa tsohon shugaban Amirka Barack Obama a shekarar 2008, wadanda suma suka yi amfani da irin wannan salo.

Frankreich Wahlen - Macrons Wahlkampf
Dan takara Emmanuel Macron yayin yakin neman zabeHoto: Getty Images/AFP/E. Feferberg

Mutumin ya ce "Ina jin cewa wannan tsarin ya yi daidai da wadda muka yi a Amirka, kuma hakan ya sanya Amirka kan hanya madaidaiciya, wanda kuma shi ne suma yanzu Faransa suka dauka suke gwadawa. Wannan na daga cikin muhimman yakin neman zabe a duniya a halin yanzu."

Paulson ba shi kadai ba ne cikin 'yan wata kasa mazauna Faransa da ke goyon bayan Macron ba. Daniel Kutt dan Jamus ne wadda ya kai shekara 15, a Faransa, duk da ya ke cewa bashi da damar yin zabe amma ya ce bai son Marine Le Pen ko Francois Fillon ya samu nasara a zaben.

"Dan takara guda daya tilo da nake gani a ido na, ya dace da yadda turai take shi ne Macron. A gaskiya yanzu haka ina jin dadin yadda lamura suke tafiya a Turai, ko da ma kuwa a ce hakan ba daidai bane. Ina ganin hanyar da ta fi dacewa mu cigaba kenan .

Cikin yini guda dai wannan tawaga sai da ta bi gidaje kimanin dari tara, ta kuma samu zantawa da mutane 600.