Shirin zaben kananan hukumomin Ghana | Siyasa | DW | 04.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shirin zaben kananan hukumomin Ghana

An sauya lokacin gudanar da zaben kananan hukumomin kasar Ghana.

Hukumar zaben kasar Ghana, na sake shirin karbar sunayen masu neman takarar shugabancin kananan hukumomi da na kansiloli a fadin kasar, bayan soke zabukan da aka tsara farawa a wannan makon.

Hakan dai ya biyo bayan soke tsarin hukumar zaben kasar ne da kotun kolin kasar ta yi, sakamakon cire sunan wani dan takaran kansila na matakin majalisar karamar hukuma da hukumar zaben ta yi daga wadanda za su yi takara.

Tun farko jiya Talata aka tsara gudanar da zabukan matakan kananan hukumomi ciki har da kansilolinsu a fadin kasar ta Ghana, sai dai hakan bai yiwu ba sakamakon soke tsarin hukumar zaben kasar da kotun kolin kasar ta yi ranar a Juma'ar da ta gabata.

Kamar dai yadda rahotanni suka tabbatar kotun kasar ta soke zaben ne bayan karar da wani masunci kuma dan takaran kansila a daya daga mazabun majalisar karamar hukuma a zaben, saboda soke sunansa daga takara da hukumar zaben kasar ta yi.

Yayin da wasu ke sam barka da matakin kotun, wasu kuwa cewa suke mayar da hanun agogo baya ne.

Suma dai ana su bangaren 'yan majalisar kasar ba su ji dadin matakin soke zabukan kananan hukumomin na Ghana ba, inda tuni ma majalisar kasa ta ce za ta gayyaci shugaban hukumar zaben kasar don amsa wasu muhimman tambayoyi na majalisar.

Wannan lamari dai zai kawo tarnaki a majalisun dokokin kananan hukumomi a kasar ganin cewa a makon da ke tafe ne wa'adin jagororin da ke kan karaga zai cika a hukumance.