Shirin zaben Bayelsa a yanayin rashin tsaro | Siyasa | DW | 06.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shirin zaben Bayelsa a yanayin rashin tsaro

Yayin da ya rage kwanaki hudu a gudanar da zabe a Karamar Hukumar Ijaw ta Kudu domin kaiwa ga kammala zaben kujerar gwamna, wasu 'yan bindiga sun yi wa wannan karamar hukuma dirar mikiya.

Yayin da ya rage kwanaki hudu a gudanar da zabe a Karamar hukumar Ijaw ta Kudu domin kaiwa ga kammala zaben kujerar gwamna a Jihar da tashe-tashen hankulan 'yan Bindiga suka haifar da tsaiko, sai gashi an bada sanarwar wasu 'yan bindiga sun yi wa wannan Karamar Hukuma ta Ijaw a jiya dirar mikiya ,tare kuma da harbe-harben firgita Jama'a.

Tashe-tashen hankula da jikkata mutane gami da kashe-kashe yayin zaben kujerar gwamna a Jihar ta Bayelsa mai jahohi 8 kacal ne ya yi dalilin dole aka soke zaben karamar hukuma daya, wato Ijaw ta Kudu. Soke zaben na wannan karamar hukuma kuma, shi ne ya sa ba a kai ga kamalla zaben na gwamna da aka gudanar a ranar 5 ga watan Disemba na bara. An dai karkashe tare da jikkata mutane a wannan zabe.

Hukumar zabe jihar Bayelsa ta tsaida ranar zabe

To a yanzu dai bayan ban iska, hukumar zabe mai zaman kanta a Jihar ta sa ranar Asabar mai zuwa, inda ake sa ran sake gudanar da wannan zabe na Karamar Hukumar ta Ijaw ta kudu da Jam'iyyu biyu musamman APC da PDP ke tada jijiyar wuya a kai, da kuma karin wasu mazabu a wasu sassan Jihar da suma aka soke.

Sai dai kuma ziyarar da na kai Jihar ta Bayelsa na fahimci cewar har yanzu fa akwai sauran rina a kaba, na dangane da yiwuwar sake shirya wannan zabe cikin nasara, ba tare da wani tashin hankali ba.

Ina jin gararin da ke kasa ne ya sa gwamnan jihar Seriake Dicsen da ke sake takara a Jam'iyyar PDP ya kira wani taron 'yan jarida na kasa da kasa da nufin bayyana halin da ake ciki na tsaro gab da ranar ta zabe.

"Dole mu tuna baya na hare-hare da aka kai wa magoya bayanmu, duka hare-hare na tada hankula, da kone-konen dukiyoyi da harbe-harbe a kai a kai, gami da garkuwa da akan yi da mutanemmu, wadda ku kanku kuna sane yanzu masu kada kuri'a na fargabar fitowa zabe" .

Gwamnan jihar Bayelsa na zargin jami'yyar APC

Gwamna Seriake Dicsen dai ,da ya yi zargin cewar jam'iyyar APC na amfani da karfin gwamnatin tarayya ta APC, ya yi ikirarin cewar shi ne ya lashe zaben da aka gudanar na kananan hukumomi bakwai, kuma ya ce shi ke da rinjaye a ragowar karamar hukumar da ta rage.

To ganin cewar gwamna shi ne da ragamar kula da tsaro a jiharsa, tare da la'akari da sarewar da gwamnan ya yi kan lamarin tsaro, da alamu lamarin na da tada hankali.

To sai dai kuma fa, shi dan takarar gwamnan na Jamiyyar APC Chief Timipre Sylva, ya bayyana a wani taron kamfe dinsa labudda shi ne zai lashe wannan zabe.

" Yayin da abokanai suka mara maka baya to akwai nasarar, sannan in har 'yan uwanka suka mara maka baya to nasara ce, dan haka Jamiyyar APC a yau ta kammala".

Na dai ji maganganu da daman a bayan fa masu matikar kada zuciya na dangane da wannan zabe da ake dako, cewar 'yan bindiga sun sake wani tanadin kassara wannan zabe kuma ma, ta hanyar tada hankula. A takaice ma, akwai bayanin cewar ko a ranar Talatar da ta gabata wasu 'yan bindiga suka yi wa wannan karamar hukuma dirar mikiya, inda kuma su ka yi ta harbe-harbe na firgita Jama'ar garin na Ijaw ta Kudu din, kuma hakan na zuwa ne a lokacin da ya rage kwanaki hudu a gudanar da wannan zabe.

Da na yi tattaki ofishin Kwamishinan Zabe na Jihar Mr Barito Kpaghi, ya nunar mini cewar ihin dinsa ko wane iri ne kan haifar da karin rudami, dan haka na tara ana gobe zabe. Kuma yanayin bayanin nasa, ya nunar gaskiya akwai matsalar tsaro sosai a kasa.

Sai dai kuma, a bayyane take cewar, a duk lokacin da aka tuntubi jamian tsaro kan wata matsala ta tsaro, sukan nunar cewar a tsaye suke. Alhaji Musa saidu,Dan Jamiyyar PDP ne.

"Akan dai tara kimimin jami'an 'yan sanda da sojojin ruwa da na kasa da na sama yayin duk zaben da za a yi a jihar, to saidai hakan har yanzu bai sa ta sake zane, dukkuwa ma da cewar akan turo dubban jami'an tsaran aikin na musamman kan zaben, ba a da wadanda ke a kasa tuni.

Kalubale dai da ke tattare da aikin tsaro a wannan shiyya ta Ijaw ta Kudu da ke kan ruwa, da kuma makwabtar teku, ba karami ba ne.

Sauti da bidiyo akan labarin