Shirin zaɓe a Zimbabwe | Labarai | DW | 07.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shirin zaɓe a Zimbabwe

'Yan adawar Zimbabwe sun ce ba da son ransu suka ƙaddamar da yaƙin neman zaɓe ba domin har yanzu babu sauye-sauyen da za su tabbatar da zaɓe cikin walwala da adalci

Zimbabwe President Robert Mugabe, left, talks to Morgan Tsvangirai, Zimbabwe Prime Minster after the swearing in ceremony of new ministers at State House in Harare, Thursday, June, 24, 2010. (ddp images/AP Photo/Tsvangirayi Mukwazhi)

Robert Mugabe da Morgan Tsvangirai

Firaministan Zimbabwe, Morgan Tsvangirai ya ce cikin takaici yake ƙaddamar da yaƙin neman zaɓenshi, inda ya ke ƙorafin cewa ko ɗaya babu wasu sauye-sauyen da aka yi na tabbatar da cewa zaɓukan na 31 ga wannan watan na Yuli ciki za su kasance cikin walwala da adalci.

Al'ummar Zimbabwe na da kusan ƙasa da makonni uku ta koma runfunan zaɓe domin ta kawo ƙarshen gwamnatin gamin gambizar Shugaba Robert Mugabe da Firaminista Morgan Tsvangirai wanda aka tilasta musu bayan tarzomar da ya biyo bayan zaɓukan shekarar 2008.

Tun ranar Juma'a Mugabe, wanda ya shafe shekaru 33 a kujerar mulkin ƙasar ya ƙaddamar da yaƙin neman zaɓensa tare da magoya baya fiye da dubu 20, ya kuma yi barazanar ficewa daga ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen kudancin Afirka wato SADC, idan har ta matsa musu lamba su ɗage zaɓen-abin da Tsvangirai ya ce ba shi da 'yancin yi, kasancewar ƙungiyar ce ƙasar ta fi dogaro da ita wajen samun tallafi.

Mugabe ne ya sanya ranar zaɓen a kan ranar 31 ga watan Yuli kuma kotun tsarin mulkin ƙasar ta mara mi shi baya, duk da cewa Tsvangirai ya buƙaci a ɗage zaɓen da watanni uku domin a gudanar da sauye-sauyen da za su rage sa bakin sojoji a zaɓen, a kuma tantance yawan waɗanda suka cancanci kaɗa ƙuri'a.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Halima Balaraba Abbas