1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali Wahlkampf

February 5, 2013

Jam'iyun siyasa a Mali sun fara shirin zaɓe bayan sanarwar shugaban ƙasa na yiwuwar kaɗa ƙuri'a kamin ƙarshen watan Juli

https://p.dw.com/p/17YFX
REFILE - CORRECTING IPTC CREDIT France's President Francois Hollande (2nd L) joins hands with Mali's interim president Dioncounda Traore after Traore spoke at Independence Plaza in Bamako, Mali February 2, 2013. France will withdraw its troops from Mali once the Sahel state has restored sovereignty over its national territory and a U.N.-backed African military force can take over from the French soldiers, Hollande said on Saturday. REUTERS/Joe Penney (MALI - Tags: POLITICS CONFLICT)
Hoto: Reuters

A yayin da sojojin Mali tare da taimakon takwarorinsu na Afrika da Faransa ke gwagwarmayar ƙwato yankin arewacin ƙasar,gamayyar ƙasa da ƙasa ta shiga tunanin hanyoyin taimakawa Mali ta kuɓuta daga halin da ta stincin kanta.

Daya daga hanyoyin cimma wannan mataki shine shirya kyakkyawan zaɓe, domin maida ƙasar bisa inganttatar turbar demokraɗiyya.

Kasar Mali ta jima ta na fama da rigingimu iri-iri, kamo daga tawaye zuwa juyin mulki wanda ke maida hannun agogo baya a yunƙurin cigaban wannan ƙasa.An sha rattaba hannu kan yarjeniyoyi tsakani 'yan tawaye da gwamnatin Bamako amma kuma daga baya ciwo ya kuma ɗanye.Saidai a wannan karo gwamnatin riƙwan ƙwraya ta bulo da wata taswira ta shirya zaɓe wanda a tunanin Badié Hima shugaban reshen yammacin Afirka na ƙungiyar ƙasa da ƙasa mai kula da girka tsarin Demokraɗiya wato NDI, shirya zaɓe na gari itace mafita ga duk

Hima:" Shirya zaɓe mai tsafta itace, hanya ta gari,ta magance duk wasu fitintinu, sannan itace ke bada damar samun hanɗin kan 'yan ƙasa.

Badiè Hima, Leiter des Nationalen Demokratie Instituts Fotograf: Katrin Gänsler Aufnahmedatum: 19. Januar 2013 Aufnahmeort: Bamako, Mali
Badie Hima shugaban NDI a MaliHoto: DW/K. Gänsler

Taswirar da gwamnatin riƙwan ƙwarya ta gabatar wadda kuma Majalisa ta amince da ita ta haramtawa hukumomin riƙwan ƙwaya su shiga takara a zaɓɓuɓukan da za a shirya."

Wannan sabuwar taswira ta yi tanadi na mussamman a matsayin riga kafi ga wariyar da ake zargin hukumomin Mali na nuna ga ƙananan ƙabilun ƙasar ko kuma ga 'ya'ya mata a cikin harkokin mulki.Daga jimlar 'yan majalisar dokoki mai ci yanzu su 147,15 ne kaɗai 'ya'ya mata.

Shugaban riƙwan ƙwarya na ƙasar Mali Pr.Dioncounda Traoré ya yi alƙawarin shirya zaɓen gama gari nan da ƙarshen watan Yuli na shekara da mu ke ciki da zaran dai haɗin gwiwar dakarun ƙasa da ƙasa su ka yi nasara 'yanto yankin arewacin ƙasar.

A lokacin da ya kai ziyara aiki ƙarshen makon da ya gabata a Mali shugaban Faransa Francois Hollande, ya yi kira ga al'umar Mali su ba maraɗa kunya ta hanyar shirya zaɓe na gari:

"Cikkaken zaɓe shine tushen girka demokradiya, ku shirya zaɓe mai tsafta aranar 31 ga watan Juli, ku nuna duniya cewar Mali na matsayin zakaran gwajin dafi a Afrika, ta fannin tsarin demokraɗiya.Gamayyar ƙasa da ƙasa na tare da ku."

Duk da cewar Mali na cikin yanayin yaƙi ,amma ga alamu jam'iyun siyasa a shiyre suke su fuskanci zaɓe kamar yadda Annette Lohmann shugabar Gidauniyar Friedrich- Ebert Stiftung reshen Mali ta baiyana:

"Duk da cewar ba a shiga gadan-gadan ba yaƙin neman zaɓe,to amma an riga an san 'yan takara da dama, wanda za su fafatawa a zaɓen shugaban ƙasa, sannan wasu jam'iyun sun yi kwaskwarima ga dokokinsu domin daidaita su da sabuwar taswirar zaɓen".

Malian soldiers stand guard in a Malian army pickup truck mounted with a machine gun in Diabaly January 26, 2013. REUTERS/Joe Penney (MALI - Tags: MILITARY CIVIL UNREST POLITICS CONFLICT)
Sojojin MaliHoto: Reuters

Da dama daga sannanun 'yan siyasar Mali, ba su da 'yancin shiga zaɓen, kasancewar su membobi a cikin hukumomin riƙwan ƙwarya.To saidai kuma tuni an riga an san sunayen wasu daga cikin mahimman 'yan takara a zaɓen shugaban ƙasa.To saidai shi kansa wannan zaɓe ya dogara kusan kacokam,ga taimakon da Mali za ta samu daga gamayyar ƙasa da ƙasa domin ɗaukar yaunin gudanar da tsare-tsare daban-daban.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Usman Shehu Usman