Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
A cikin shirin za a ji cewa a Najeriya jam'iyyar adawa ta PDP ta dauki hanyar dinke rikicin cikin gida da ya kunno mata, a Nijar sabin membobin hukumar koli mai kula da kafafen sadarwar kasar watau CSC sun sha rantsuwar kama aiki.
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, ya kaddamar da matatar man fetur ta Dangote a Ijebu Lekki a birnin Legas, matatar da ke iya sama wa sama da mutum dubu 100 aikin yi.
Gwamnatin Najeriya ta bayyana damuwa a kan yaduwar kananan makamai a tsakanin jama'a ganin yadda hakan ya ke da illa musamman ga mata da kananan yara.
Mabiya addnin Kirista a fadin duniya na gudanar da bukukuwan Kirsimeti da suka saba gudanarwa duk shekara, a wani mataki na tunawa da Yesu Al-masihu.
Sashen Hausa na DW na gabatar muku da wasannin kwallon kafa na lig-lig na Jamus wato Bundesliga kai tsaye ta rediyo.