Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta gabatar da kudirori da manufofin Jamus na shugabancin karba karba na majalisar Tarayyar Turai.
Jamus na ci gaba da zawarcin kwararrun ma'aikata 400,000 a kowace shekara don cike gibin da take da shi a fannin kwadago sakamakon tsufar al'umma. Galibin ma'aikatan da ke shigowa Jamus daga ketare suna sake ficewa.
Kasar Chaina ta yi kira ga kasashen Rasha da Ukraine da su hau teburin tattaunawa don sasanta rikicin da suka shafe shekara guda suna yi a maimakon ci gaba da amfani da makamai.
Baya ga amincewa da kakabawa Rasha sabon takunkumi da shugabannin kasashen kungiyar EU suka yi, sun kuma amince da ci gaba da bai wa Ukraine tallafin kudi da yawansu ya kai Euro biliyan 18.
Shugaba Bashar al-Assad na Siriya na kokarin ganin kasarsa ta fita daga matsayin saniyar ware a tsakanin al'ummomin kasa da kasa.