Shirin tunkarar Jam′iyyar PDP mai mulki a Najeriya a zaben kasar da ke tafe | Siyasa | DW | 18.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shirin tunkarar Jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriya a zaben kasar da ke tafe

Tun dai da jam'iyyar adawa ta APC ta gudanar da zaben fidda gwaninta inda ta zabi Janar Buhari mai ritaya , wannan zabi dai ya zama kalubale ga jam'iyyar PDP mai mulki a zaben 2015.

Al'umma da dama dai musamman daga arewacin Najeriya na ganin salon mulkin na jam'iyyar ta PDP da gazawa wajen kare kare rayuka da dukiyoyin al'umma ballantana a je ga batun bunkasar tattalin arzikin na daidaikun jama'a.

DW.COM