Shirin tsagaita wuta a Ukraine ya fara aiki | Labarai | DW | 15.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shirin tsagaita wuta a Ukraine ya fara aiki

Bangaren gwamnatin Ukraine da kuma na 'yan awaren gabashin kasar ba su yi sabon fada tsakaninsu ba tun sa'ilin da yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a ranar Lahadi.

Shugaba Petro Poroshenko ya umarci dakarun sojan kasar su mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar tun daga misalin karfe goma agogon GMT kamar yadda aka cimma a yarjejeniyar birnin Minsk bisa jagorancin Rasha da Jamus da Faransa.

Kamar yadda wakilin kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya bayyana babu sabon fada tun sa'ilin da yarjejeniyar tsagaita wutar ta fara aiki.

Ana ci gaba da sanya idanu kan shirin tsagaita wuta a rikicin kasar Ukraine tun da sanyin safiyar yau Lahadi duk da irin zargin mahukuntan birnin Kiev da Amirka cewa Rasha na iza wutar rikici na baya bayanan ta yadda bangaren 'yan awaren zai kara fadada yankunan da ke karkashinsa kafin cikar wa'adin fara aiki da shirin tsagaita wutar.