Shirin Taba Ka Lashe | Zamantakewa | DW | 23.04.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Shirin Taba Ka Lashe

Ko kasan cewa akwai alaka mai karfi tsakanin masarautun gargajiya da mafarauta a nahiyarmu ta Afirka? A shirin Taba Ka Lashe na wannan mako ya yi nazari kan wannan alaka.

Saurari sauti 09:49

Alaka tsakanin masarautun gargajiya na Afrika da mafarauta, alakace da ta samo asali tun  iyaye da kakanni, domin kai ana iya cewa mafarauta ne suka kafa garuruwa da dama a yayin tafiye-tafiyensu na harbi. Birnin Zinder da ake kira Damagaram na daga cikin manyan masaurantun gargajiya masu dumbun tarihi a jamhuriyar Nijar kuma mafarauta suka kafa shi  shekaru da dama da suka gabata kafin zuwan sakin farko Malam Yunus a 1731. Domin martaba wannan al'ada da ke zaman ginshiki a tarihin birnin na Damagaram an shirya  wata kasaitattar haduwar ''Maharban Afrika'' wacce aka yi wa taken ''Festival international des Chasseurs''.