Shirin soma gasar cin kofin Turai a Faransa | Labarai | DW | 10.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shirin soma gasar cin kofin Turai a Faransa

Yayin da ake soma gasar cin kofin Turai na kwollon kafa a kasar Faransa, hukumomin kasar sun tashi tsaye wajen ganin komai ya tafi kamar yadda aka tsara.

Ministan kwadago kasar ta Faransa Myriam El Khomri, ta tabbatar a wannan Juma'a cewa, a shirye take ta gana da Philippe Matinez, shugaban kungiyar kwadago ta CGT idan har hakan zai taimaka wajen dage wannan yajin aiki. Sai dai a cewar Jean Pierre Lalbat shugaban kungiyar ma'aikata masu ritaya na kungiyar ta CGT suna nan kan bakansu.

Hukumomin Faransa dai na ci gaba da bin matakai na ganin 'yan kallon kwallon kimanin dubu 80 duk sun samu zuwa kallo duk kuwa da yajin aiki a bangaren na sufuri.