Shirin samar da sabuwar doka a Ukraine | Labarai | DW | 16.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shirin samar da sabuwar doka a Ukraine

Wannan doka da shugaba Poroschenko ya mika wa majalisa, ta tanadi karawa wasu yankunan yankin gabashin kasar iko bisa tanadin yarjejeniyar sulhu.

Majalisar dokokin Ukraine ta amince da wata dokar da ta tanadi kara wa gwamnatocin yankunan Donetsk da Luhansk iko - yankunan da gabashin kasar da ke goyon bayan Rasha . Da ma dai wannan doka, na daya daga cikin sharuddan da aka gindaya a yarjejeniyar tsagaita wutar da bangarorin suka rattabawa hannu a watan Fabrairu, kuma ta tanadin yin hakan ne a matsayin mataki na din-din-din kafin karshen wannan shekara ta 2015.

'Yan majalisa 288 suka amince da wannan doka wanda yanzu za a mika ta ga kotun kundin tsarin mulki, kafin a sake karanta ta a majalisa, inda za ta bukaci amincewar akalla mutane 300. Shugaba Petro Poroschenko ne ya gabatar da kudurin dokar, kuma matakin yana samun goyon bayan kasashen yamma. Kamfanin dillancin labaran Jamus ya rawaito cewa hatta mataimakiyar sakataren kula da harkokin da suka shafi Turai da Asiya Victoria Nuland ta kasance a majalisar.