Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
A cikin shirin za a ji a kasar Burkina Faso garkuwa da mutane da yan bindiga ke yi na daukar wani salo da ke neman haddasa rudani a yammacin Afirka.
Mahukunta a Burkina Faso sun sanar da fara bincike a kan zargin da ake yi wa dakarun sojinsu na kisan wasu 'yan Najeriya da ke kan hanyar su ta zuwa birnin Kaolaha na kasar Senegal.
Hadin gwiwar hukumomin yaki da cin hanci da rashawa a Afirka ta Yamma sun gana a birnin Yamai inda suka yi don duba matsalar a cikin kasashen yankin da ma nazarin yadda za a hada karfafa musayar bayanai.
Mutane hudu da suka hada da jami'an tsaro biyu sun rasa rayukansu sakamakon harin ta'addanci a kasar Burkina faso da ke yankin yammacin Afirka.
Maharan da ake kyautata zato masu ikrarin jihadi ne sun kashe gwamman fararen hula a wani kazamin harin da suka kai a arewacin Burkina Faso iyaka da Nijar