Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
A cikin shirin za a ji cewa a birnin Cologne na Jamus sama da masu zanga-zanga 50,000 za su yi taro. Amirka da Ostareliya za su hada kai a fanin tsaro da musayar 'yan gudun hijira.
Jamus ta mika wa Ukraine wasu sabbin makamai da ke dauke da na'urori masu iya dakile duk wasu hare-hare da makamai masu linzami daga abokiyar fadanta Rasha.
Yayin da fada ke dada rincabewa a Khartoum babban birnin kasar Sudan, jiragen saman sojan Jamus uku na farko da suka fice daga Sudan sun isa kasar Jordan, wani jirgin iso da sauran mutane birnin Berlin.
An shirya shugabannin biyu za su tattauna batun kara ba da makamai ga Ukraine wadanda suka hada da tankokin yaki masu sulke.
Jamus na ci gaba da zawarcin kwararrun ma'aikata 400,000 a kowace shekara don cike gibin da take da shi a fannin kwadago sakamakon tsufar al'umma. Galibin ma'aikatan da ke shigowa Jamus daga ketare suna sake ficewa.