Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Shirin ya kunshi labaran duniya da waiwayen wasu manyan batutuwan da suka wakana a nahiyar Afirka a wannan makon mai karewa. Sudan ta amince da sake dawo da hulda da kasar Isra'ila. ICC ta ja kunne game da rikicin kasar Guinea Conakry.
Tura sakon Facebook Twitter Whatsapp Web EMail Facebook Messenger Web
Permalink https://p.dw.com/p/3kNUw
A karon farko bayan sabunta dangantaka a tsakanin juna, jirgin fasinjan Hadaddiyar Daular Larabawa na Flydubai ya soma jigilar fasinjoji daga Isra'ila zuwa birnin Dubai a wannan Alhamis.
Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya soki Sudan bisa amincewar da ta yi da Isra'ila a matsayin abokiyar hulda. A wannan Juma'ar ce kasashen biyu suka kulla yarjejeniyar dawo da dangantaka a karkashin jagorancin Amirka.
Masana a yankin Gabas ta Tsakiya sun ce yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma tsakanin Isra'ila da Sudan aba ce da za ta amfani kasashen biyu har ma da Amirka da ta shiga tsakani da aka kai ga cimma matsayar.
Zabne shugaban kasa a Tanzaniya da batun huldar diplomasiyya tsakanin Sudan da Isra'ila da ma batun zanga-zangar #EndSATS a Najeriya, sun dauki hankulan jaridun Jamus na wannan makon.