Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Bayan kun saurari Labarai muna tafe da rahoton jawabin wata jami'ar sa kai game da yanayin da wasu yan matan Chibok ke ciki a hannun mayakan Boko Haram .
'Yan matan Chibok biyu da sojoji suka ceto ne suka shaida wa 'yan jarida yadda Boko Haram ta yi musu auran dole. A cikin daji ne dai sojojin suka samu matan, kowacce da karamin yaron da ta haifa wa dan Boko Haram.
Daya daga cikin 'yan matan makarantar Chibok da mayakan Boko Haram suka sace sama da shekaru bakwai a jihar Borno, ta koma cikin iyayenta bayan mika kanta da mijinta ga jami'an tsaron Najeriya.
Bayan mika wuya da wasu cikin wadanda suka sace 'yan mata 'yan makarantar sakandaren garin Chibok a Najeriya suka yi, wasu kungiyoyi na kira da a tabbatar an hukunta 'yan bindigar da suka yi sace su.
Ana kyautata zaton mayakan Kungiyar ISWAP ne suka yi garkuwa da ma'aikatan gwamnatin jahar Borno shida daga yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya.