Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
A cikin shirin za a ji cewa a Najeriya kananan Jam’iyyun na ci gaba da narkewa suna komawa ga manyan Jam’iyyun da ake sa ran za su kai labari a zaben kasar, a Nijar ta'addanci na neman durkusar da aikin hakar ma'adanai a yanmacin kasar.
Gwamnatin Najeriya ta bayyana damuwa a kan yaduwar kananan makamai a tsakanin jama'a ganin yadda hakan ya ke da illa musamman ga mata da kananan yara.
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, ya kaddamar da matatar man fetur ta Dangote a Ijebu Lekki a birnin Legas, matatar da ke iya sama wa sama da mutum dubu 100 aikin yi.
Mabiya addnin Kirista a fadin duniya na gudanar da bukukuwan Kirsimeti da suka saba gudanarwa duk shekara, a wani mataki na tunawa da Yesu Al-masihu.
A wannan Litinin aka bude babban taron kasa da kasa a birnin Yamai na kasar Nijar don nazari kan yadda za a sake gina yankin Tafkin Chadi da rikicin Boko Haram ya daidaita.