Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
A cikin shirin za a ji cewa a Najeriya, Babban Bankin kasar CBN ya karyata cece-kucen da ake yi kan kudin da aka tara a matsayin harajin hatimin kan sarki. A Jamhuriyar Nijar kuwa, gamayyar kungiyoyin kwadago na ITN sun fara yajin aiki.
Gwamnatin Najeriya ta bayyana damuwa a kan yaduwar kananan makamai a tsakanin jama'a ganin yadda hakan ya ke da illa musamman ga mata da kananan yara.
Rahotanni daga Najeriya na cewar wasu masu zanga-zanga a birnin Abeokuta da ke jihar Ogun a kudancin kasar sun kai hari a wasu manyan bankuna tare da kona tayoyi a kan tituna.
Ana yajin aiki na kwanaki biyu da gamayyar kungiyoyin kwadago na Jamhuriyar Nijar suka kira kan rashin cika wasu bukatu da suka amince da gwamnati.
Babban bankin Najeriya wato CBN ya karyata labarin cewa ya bayar da izinin ci gaba da karbar tsofaffin takardun kudi na Naira 1000 da 500.