Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
A ciki za a ji labarin wata ziyarar da mataimakin shugaban majalisar da ke mulki a Sudan yake yi a Habasha. An ceto wasu bakin haure a tsibirin Lampedusa na Italiya.
Jiragen ruwan Italiya sun gano gawar mutane biyar da suka mutu a lokacin da suke kokarin tsallaka tekun Bahar Rum a cikin jiragen ruwa marasa inganci.
Dakarun kasar Sudan suna tuhumar sojojin Habasha da kashe jami'an tsaronsu guda bakwai da farar hula daya, wadan da aka kashe suna cikin mutanen da aka yi garkuwa da su.
Ministan kiwon lafiyar kasar Jamal Nasser ya ce duk da jami'an tsaro sun taimaka wurin dakile rikicin kabilancin, kawo yanzu mutane 291 lamarin ya raunata.
Daruruwan Hausawa sun taru a birnin Khartoum a wannan Talata domin yin tir da rigingimun kabilanci tsakaninsu da kabilar Bartis wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 79 a karshen makon jiya.