Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Cikin shirin akwai batun hari da 'yan ta'adda suka kai garin Makalondi da ke Nijar. Sai fargabar da ake bayyanawa na rashin tsaro lokacin Kirsimati a Nijar. Akwai zazzabin Lassa da ya salwantar da rayuka a jihar Bauchin Najeriya.
Akasarin jaridun Jamus sun yi sharhi kan shagulgulan bikin rantsar da sabon shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.
A Jamhuriyar Nijar matsalar tsaro a yankin magangamar iyakoki uku na kasar da Mali da ma kasar Burkina Faso na kara kamari, lamarin da ya fara tayar da hankalin direbobi da ma matafiya.
A Burkina Faso dubban mutane sun yi zanga-zanga, inda suke neman gwamnati ta kara azama wurin kare su daga hare-haren masu ikirarin jihadi.
A karon farko a nahiyar Afirka, shugaban gwamnati da mambobin majalisarsa sun yi marabus saboda matsin lamba daga al'umma a Burkina Faso.