A cikin shirin bayan an ji labaran duniya za a ji cewa a Najeriya gwamnatin Kaduna ta gargadi wadanda suka wasaseshen abincin tallafin jama'a da su dawo da shi saboda akwai cimakar da ke kunshe da guba. A Jamhuriyar Nijar bangaren Malam Hama Amadou a babbar jam'iyyar adawa ta Lumana Afirka ya ce ko ana ha maza ha mata jagoran jam’iyyar sai ya tsaya takara a zaben shugabancin kasar da ke tafe.