Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
Sarki Charles na III na Birtaniya ya iso nan Tarayyar Jamus don fara ziyarar aiki ta tsawon kwanaki uku, inda zai gana da shugaban gwamnatin kasar Olaf Scholz da sauran kusoshin gwamnati.
Yawan mutanen da ke shiga kasar Birtaniya da nufin zama ya kai kololuwa da sama da mutum dubu dari shidda, a cewar alkaluman da kasar ta fidda a yau.
Wata kotu a birnin London ta yanke wa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ike Ekweremadu hukunci bisa laifin safarar wani matashi da nufin cire kodarsa.
Akwai yiwuwar Rasha ta sake fuskantar wani salon takunkumin tattalin arziki daga kasashe masu karfin arzikin masna'antu na G7, a bangaren ma'adanin lu'u-lu'un da take da arzikinsa.
Masana kimiyyan sun ce wannan nasara ce da bincikensu na shekaru 30 ya samo tun bayan da suka dukufa lalubo rigakafin cutar maleriya da a duk shekara ke kashe mutum kimanin 600,000, galibi kananan yara a kasashen Afirka.