Shirin Osthoff na komawa Iraki | Siyasa | DW | 27.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shirin Osthoff na komawa Iraki

Susanne Osthoff ta ce zata sake komawa bakin aikinta a Iraki

Susanne Osthoff

Susanne Osthoff

Susanne Osthoff ta dage lalai sai ta sake komawa Iraki, kamar yadda ta fada a cikin wata hira da gidan telebijin na Aljazeera yayi da ita a jiya lahadi, ko da yake ba ta fadi ranar da take da niyyar komawar ba. Amma ta ce ba makawa ta sake komawa bakin aikinta na tone-tonen kayan tarihi. Wani abin da aka lura da shi a hirar da gidan telebijin din na Aljazeera yayi da ita shi ne kasancewar jami’ar ta kasance cikin rudu da rashin sanin tabbas. Bayan fara hirar da aka yi da ita da larabci, daga baya Susanne Osthoff ta nemi tafinta, saboda ga alamu bata fahimci ainihin tambayoyin da ake mata ba. Ta ce a hakika ta ga kabari kusa. Kuma a cikin makonni ukun da aka yi garkuwa da ita, an rika ciniki da ita ne daga wannan gungu zuwa wancan. Kome ya tafi ne a cikin kiftawa da Bisimillah a lokacin da aka sace ta a ranar 25 ga watan nuwamban da ya wuce. Masu alhakin garkuwa da ita sun jefa ta ne a bayan wata mota suka kuma yi tafiya ta kusan awa daya a motar, inda suka isa wani gidan ba babu kowa a cikinsa. Ta ce masu alhakin garkuwa da ita sun bayyanar mata a fili cewar ita wata muhimmiyar kawa ce ga al’umar Iraki, amma sun tsare ta ne saboda wasu dalilai na siyasa. Kuma babu wani dalili na tsoro da rudami, ba wani abin da zai shafi lafiyarta, musamman ma saboda kasancewarta musulma. Sun dai nuna mata so da kauna tsawon makonni uku da tayi a hannunsu.

Ga alamu kuwa kwalliya ta mayar da kudin sabulu a game da garkuwa da ita da suka yi. Domin kuwa ko da yake ba a biya diyya ba, amma akalla gwamnatin Jamus tayi musu alkawarin gina musu makarantu da gidajen asibiti.

Ministan harkokin waje Frank-Walter Steinmeier yayi kira ga malamar tone-tonen kayan tarihin mai shekaru 43 da haifuwa da ka da ta koma Iraki, inda ya ce bayan makonni uku da aka yi ana kai ruwa rana domin neman sakinta, a hakika abin takaici ne in ji cewar wai Susanne Osthoff na da niyyar sake jefa kanta da kanta cikin wata sabuwar barazana, a cewar ministan harkokin wajen na Jamus. Tuni dai gwamnati ta ba da sanarwar cewar ta kakkabe hannuwanta daga dukkan shirye-shirye na bincike da malamar ke gudanarwa a Iraki.