1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin nukiliyar Iran

Pinado Abdu WabaJuly 23, 2015

Shugaban ya jaddada mahimmancin yarjejeniyar bacin yadda masu ra'ayin mazan jiya a kasar ke sukarta suna zargin za ta kasance hatsari ga tsaro.

https://p.dw.com/p/1G3j8
Iran Militärparade in Teheran Präsident Rohani
Hoto: AFP/Getty Images/B. Mehri

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani, ya kare yarjejeniyar nukiliyar da kasarsa ta cimma tare da Turai, inda ya soki masu ra'ayin mazan jiyan kasar wadanda ke nuna adawa da sabon matakin, yana mai cewa yarjejeniyar ta bayyana abin da 'yan kasar ke muradi ne, kuma wannan ya fi mahimmanci a kan cece-kucen cikin gida dangane da gundarin abin da yarjejeniyar ta kunsa.

Bisa bayanan kamfanin dillancin labaran Reuters dai, sojojin juyin juya halin kasar wadanda suke da tasiri sosai a batutuwan siyasa da tattalin arziki da tsaron kasar ne, suka fi sukan shirin, da hujjar cewa babban hatsari ne ga tsaron Iran.

A karkashin wannan yarjejeniya ta 14 ga watan Yuli, za a rika janyewa Iran takunkumin da aka kakaba mata sannu a hankali, a yayin da a waje guda kuma ake kokarin takaita shirinta na makamashin nukiliya wanda tun da dadewa Turai ke zargin cewa na hada-hada makaman kisan kare dangi ne, zargin da ta karyata.