1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Tirka-tirka kan shirin nukiliyar Iran

Binta Aliyu Zurmi RGB
April 14, 2021

Batun nukiliyar kasar Iran ya sake dawowa a matsayin wani babban kanun labaran kafafen yada labaran duniya a yayin da kasashen yamma ke kokarin komawa kan yarjejeniyar da aka cimma da Iran a shekarar 2015.

https://p.dw.com/p/3rwpq
Iran Atomprogramm
Hoto: Iranian Presidency Office/AP Photo/picture alliance

A yanzu haka dai batun nukilyar kasar Iran ya sake dawowa a matsayin wani babban kanun labaran kafafen yada labaran duniya a yayin da kasashen yamma ke kokarin komawa kan yarjejeniyar kasar Iran da aka cimma, wacce ta takaita karfin makashin nukuliyan Iran, yarjejeniyar da tsohon Shugaban Amirka Donald Trump ya yi fatali da ita. Sabon Shugaban kasar Amirka Joe Biden ya nuna anniyarsa ta komawa kan yarjejeniyar, sai dai kawar Amirka Isra'ila na matukar adawa da hakan. Kasashen Turai dai sun yi maraba da shirin Shugaba Biden na dawowa kan yarjejeniyar da aka cimma a lokacin mulkin Shugaba Barack Obama, wace ta samu amincewar takaita nukilyar Iran. Inda tuni bayan hakan wasu kasashen yamma suka fara dira a kasar Iran don zuba jari, sai dai shekaru kadan, bayan da mulkin Obama ya kare, hannun agogo ya koma baya, kasashen Turai da suka zuba jarinsu a Iran suka rasa na yi, bayan da babbar kawar Turai wato Amirka ta zabi Shugaba Trump wanda ba ya mutunta kowa illa kansa.

Karin Bayani:  Nukiliyar Iran: Fargabar fadawa cikin tashin hankali

Iran Sergej Lawrow in Teheran
Ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov da takwaransa na Iran Javad ZarifHoto: Russian Foreign Ministry Press Service/AP/picture alliance

Zuwan Shugaba Joe Biden ya kasancewa Turai a matsayin wata babbar dama ta warware rikicin nukilyar Iran. To sai dai itama Iran a bangarenta akwai rashin hakuri, inda ta yi ta kara yawan karfin nukilyarta, kana a ranar Litinin din da ta gabata, ta sanar da soke wasu huldodinta da Turai, a nata bangaren, Tarayyar Turai ta sanar da aza takunkumi kan wasu jami'an gwamnatin Iran wadanda ake ganin suna taka rawa wajen cin zarafin al'ummar Iran. Rasha wacce ke babbar kasa da ke dasawa da Iran, ta yi gargadi ga duk wani manakisa da zai sa a hana komawa ga yarjejeniyar nukilyan Iran.

Karin Bayani:  Batun nukiliyar Iran da wasu kasashen Turai

Israel Premierminister Benjamin Netanjahu
Iran ta dora alhakin harin Natanz a kan Isra'ila Hoto: Abir Sultan/AFP/Getty Images

Sai dai gabanin wannan sanar da sabbin takunkumaida Tarayyar Turai ta yi kan wasu jami'an gwamnatin Iran, an jiyo ita kanta Kungiyar EU na Allah wadai da duk wata manakisar da za ta hana farfado da yarjejeniyar nukilyar ta Iran, musamman bayan da Iran ta sanar da wani harin yanar gizo da aka kai wa tashar nukilyar ta, da ta dora alhakinsa kan Isra'ila, don haka shi ma Ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov, ya sake yi kalamin mai nuna sasauci da hannunka mai sanda ga kungiyar ta EU.

A karshen makon da ya gabata harin ya auku a tashar nukilyar ta Natanz, wanda ake ganin ka iya zama wani babban koma baya ga shirin komawar tattauna da Iran, inda Shugaba Joe Biden na Amirka ya amince da hada kai tare da kawayensa naEU. A yanzu haka dai sakataren tsaron Amirka na ziyara Turai inda a yau zai gana da gwamnatin Jamus, bayan kammala nziyarar da ya kai Isra'ila, ziyar da ake gani ta na kumshe ne da batutuwan nukilyar kasar Iran.