Shirin Nukiliyar Afirka ta Kudu ya ga cikas | Labarai | DW | 26.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shirin Nukiliyar Afirka ta Kudu ya ga cikas

Fadada aikin makamashin nukiliyar dai ya samu suka ta kungiyoyi da dama wadanda ke fafutikar amfani da makamashi da ake iya sabintawa.

Südafrika Atomkraftwerk Koeberg nahe Kapstadt (picture-alliance/dpa/EPA/N. Bothma)

Tashar makamashin nukiliya a wajen Cape Town

Kokarin da kasar Afirka ta Kudu ke yi na fadada shirinta da ya shafi makamashin nukiliya tare da hadin gwiwar kasar Rasha ya samu babban koma baya a wannan rana ta Laraba bayan da wata kotu a kasar ta ce shirin ya sabawa doka.

Da ta ke bayani ga kamfanin dillancin labarai na Jamus DPA, babbar kotun ta Western Cape ta ce yadda gwamnati ta rike shirin farko na makamashin ya sabawa doka don haka ta sake nazari ta kuma aje shi gefe.

Har ila yau kotun ta kuma jingine shirin hadin gwiwa tsakanin kasar ta Afirka ta Kudu da Koriya ta Kudu da Amirka kan makamashin na nukiliya. Wasu kungiyoyi na fafutikar kare muhalli ne dai suka gurfanar da gwamnatin kasar a watan Oktoba na shekarar 2015, inda suka ce yarjejeniyar da gwamnati ta kulla ba ta saurari bangaren majalisa ba wanda kuma yin hakan wajibi ne.

Fadada aikin makamashin nukiliyar dai ya samu suka ta kungiyoyi da dama wadanda ke fafutikar amfani da makamashi da ake iya sabintawa, wasu kuma na cewa kasar ta Afirka ta Kudu ba za ta iyakashe kudi Dala miliyan dubu 76 ba kan wannan aiki.