Shirin karbe makamai | Labarai | DW | 09.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Shirin karbe makamai

Dakarun Faransa sun samu gagarumar tarba daga mutanen Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya.

Dakarun kasar Faransa sun isa sassa daban-daban na kasar Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya, inda suka samu gagarumar tarba daga mazauna kasar.

Ministan tsaron kasar ta Faransa Jean-Yves Le Drian ya ce daga safiyar wannan Litinin za a fara karbe makamai daga hannun kungiyoyin tsageru, kuma sojojin za su yi amfani da karfi muddun suka samu turjiya. Kimanin dakaru 1,600 na Faransa ke tallafa wa dakarun kasashen Afirka, kuma isar sojojin na Faransa ya janyo lafawar lamura, inda cikin makon da ya gabata aka hallaka fiye da mutane 400 a rikicin tsakanin kungiyoyin tsageru na Kiristoci da Musulmai.

Shugaban wucin gadi na kasar ta Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya Michel Djotodia, ya yi godiya wa kasar ta Faransa bisa wannan taimako na tura dakarun domin dakile fadawar kasar cikin rikici.

Yanzu haka Kungiyar Tarayyar Turai ta tura jirgi dauke da kayayyakin agaji wanda zai rika karakaina tsakanin kasar ta Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya da kuma Kamaru mai-makwabtaka, wajen da zai rika yada zango.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu